PLATEAU PEACE BUILDING AGENCY (PPBA)

Office of the Executive Governor,
Plateau State.

...towards a Plateau at Peace with itself and the rest of the world.
PPBA

Hukumar Inganta Zaman Lafiya Ta Jahar Filato Ta Gudanar Da Bukin Sanya Hannu A Takardar Kudirin Tabbatar Da Zaman Lafiya Tsakanin Al'ummar Fulani Da Irigwe Na Kauyen Miango A Karamar Hukumar Bassa Ta Jahar Filato

Wannan Babbar Nasara Ce Ga Al'ummar Fulani Da Irigwe...

An sanya hannu a Takardar Kudirin Tabbatar da Zaman Lafiyan ne a gaban manya-manyan Shuwagabannin Jahar Filato ciki har da Gwamnan Jahar ta Filato Mai Girma Rt. Hon. Simon Bako Lalong, a Ranar Laraba 13th ga Watan Yuli, na shekarar 2022.

Manyan shaidu a wurin sanya hannun sune Babban Shugaban Hukumar Inganta Zaman Lafiya ta Jahar Filato, Mr. Joseph Lengmang; Manyan Shuwagabannin Majalisar Koli ta Addinai a Jahar Filato, Rev. Prof. Pandang Yamsat da HRH. Muhammad Sambo Haruna, wanda ya samu wakilcin Mai Girma Sarkin Kanam, HRH. Alh. Mu'azu Muhammad II; Kwamandan Operation Safe Haven, Maj. Gen. Ibrahim Ali; da Maga-Takardan Jahar Filato, Prof. Danladi Atu.

Sauran shaidun sun hada da wakilin Cibiyar Zaman Lafiya ta Kasar Amurka, Dr. Chris Kwaja; Mai Girma Mataimakin Shugaban Hukumar Zaman lafiya ta Jahar Kaduna, Dr. Sale Momale; manyan Daractocin Cibiyar Sasanta Rikicin Addinai dake da tushenta a Jahar Kaduna, Iman Ashafa da Pastor James Wuye; Prof Madaki, shugaban Cibiyar Bunkasa Cigaban Kabilun Jahar Filato; sauran shuwagabannin Majalisar Koli ta Addinai a Jahar Filato duk suna wurin don shaida sanya hannu a takardar kudirin tabbatar da zaman lafiyan da kowa ya amince da ita.

Muna addu'a da fatan wannan gagarumar nasarar da aka samu zata kawo karshen duk wata gaba, ta'adi, barnatar da dukiyoyi da zubar da jini, sa'annan ta bude sabon shafi ta hanyar yafiya da sasantawa a kasar Irigwe.

Zamu cigaba da kawo muku cikakkun bayanai dangane da wannan buki da abubuwan da takardar kudirin ta kunsa cikin kwanaki masu zuwa, tare kuma da kira zuwa ga abokanan aikinmu na inganta zaman lafiya da su cigaba da tallafawa da bayar da gudumawa ga kwamitin tsaro na cikin kasar irigwe wajen ganin an cimma nasarar aiwatar da wannan kudirin da duk aka amince dashi.