PLATEAU PEACE BUILDING AGENCY (PPBA)

Office of the Executive Governor,
Plateau State.

...towards a Plateau at Peace with itself and the rest of the world.
PPBA

Bangarorin Da Muke Yin Aiki

Rikice-rikice kamar mutane ne guda biyu (2) da baza su taba yin kamanni daidai da-juna ba. Mu a Hukumar Inganta Zaman Lafiya ta Jahar Filato, munyi kyakkyawan nazari kan rikice-rikicen da suka yi tsami na tsawon shekaru Ashirin (20) wajen mayar da hankali kan abubuwan da suka janyo, menene ya kawo su, sakamakon su da kuma matakan da aka dauka. Muna kulawa da kyau wajen gina Zaman Lafiya a cikin Al'ummar da ta tsinci kanta a cikin tashin hankali lokaci zuwa lokaci da kuma samar mata da mafita don cigaba. Domin irin dabarun mu da suka kewaye ko ina, muna mayar da hankali ne a wadannan bangarorin guda shida (6) kamar haka;

Buncike, Hadin-Gwiwa da Jagoranci

Masu aiki don inganta Zaman Lafiya suna dogaro ne da buncike a matsayin muhimmin abinda zai basu dama suyi nazari kuma su gane rikice-rikicen. Hakannan yana da muhimmanci wajen jagorantar dukkanin masu ruwa-da-tsaki domin tabbatar da samarwa da kuma dorewar shiryayyen hadin-gwiwa.

Dalilin samar da buncike, hadin-gwiwa da jagoranci a matsayin bangare na musamman don mayar da hankali, mun dauki aniyar juya gurbataccen zaman da Jahar take yi izuwa ingantacce ta hanyar buncike mai dorewa, ajiye sakamakon buncike cikin tsari, kyakkyawan jagoranci da kuma shiryayyen hadin-gwiwa.

Kulawa da Albarkatun Kasa

Babban dalilin da yasa ake yawan samun rikice-rikice a Jahar Filato yana da dangantaka da mallaka da kuma amfani da albarkatun kasa. Manufar mu itace mu kaddamar da wani tsari - a hukumance - wanda zai tabbatar da hadin-gwiwa ga duk masu ruwa-da-tsaki wajen daidaita tsari mai dorewa na amfani da albarkatun kasa domin amfanin dukkanin masu ruwa-da-tsakin a cikin Jahar Filato.

Ilmantarwa akan Zaman Lafiya

Kamar yadda wani kwararre, mai suna Paco Cascon yake fada a cikin littafin sabon karni, "Neman ilimin hanyar da za'a warware rikice-rikice cikin kyautatawa kuma ba ta hanyar rikici ba wani irin babban kalubale ne, kuma abu ne da su kansu masu ilmantarwar baza su iya kaucewa ba" Manufarmu a wajen ilmantarwa akan Zaman Lafiya itace mu bunkasa fahimta akan muhimmancin zamantakewa cikin lumana da kuma dabarun warware rikice-rikice ba tare da tashin hankali ba a wurin Al'ummar Jahar Filato.

Cigaban Jinsi da kuma Matasa

Munyi la'akari da bukatar samar da ayyuka da shirye-shiryen inganta Zaman Lafiya domin fahimtar irin bambance-bambancen Al'ummai da kuma yadda za'ayi amfani dasu. Don haka ne, muke da burin aiwatar da buncike mai zurfi akan Jinsi da matasa domin tabbatar da Ingantaccen Zaman Lafiya. Manufarmu itace mu bunkasa shigar da batun Jinsi da na matasa a cikin duk abinda ya shafi daukan mataki, tsarawa, aiwatar da ayyukan kare rikice-rikice, tabbatar da Ingantaccen Zaman Lafiya da samar da cigaba mai amfani.

Warkarwar Bayan-Rikici da Samar da Abinda-Aka-Rasa

Domin samun Ingantacciyar nasarar magance raunuka na irin abubuwan da rikici yake bari bayan kurar ta lafa, munyi kyakkyawan tsari cikin nutsuwa na irin abubuwan da zamu yi don cimma kudirin mu. Muna da burin samar da hanyoyi da matakan warkarwar bayan-rikici domin sasantawa, magancewa da kuma mayar da mutanen da rikici ya shafe su izuwa wuraren zamansu a Jahar Filato.

Dabarun Neman Tallafi

Warware rikice-rikice da wanzar da Ingantaccen Zaman Lafiya yana da bukatar kayan-aiki; na mutane, da na kudade, har ma da na albarkatun kasa. A matsayin mu na masu kulawa da dukkanin wadannan abubuwan, kudirin mu shine mu kasance hukumar da ta tattaro kwararrun mutane, kayan-aiki da kuma tallafi na kudade domin samun damar gudanan da Ingantattun ayyuka don tabbatar da Zaman Lafiya.

Mun sanya dukkanin wadannan bayanai da ma wasunsu a cikin kundin mu mai suna wanda za'a iya saukewa don karin bayani.